MAIDUGURI: Samun Mafita Ga Ta’azzarar Ambaliyar Ruwa A Najeriya
VOA Hausa VOA Hausa
94.9K subscribers
557 views
8

 Published On Sep 15, 2024

Ambaliyar ruwa da ake fama da ita a Najeriya ta haifar da babban ibtila’i da ayyukan jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 30 inji majalisar dinkin duniya.

Biyo bayan rugujewar dam na Alu da ke garin Maiduguri wanda yayi sanadi tare da ta’azzara mummunar ambaliyar, hukumomi a jihar Borno sunce mutane akalla 30 ne suka rasa rayukan su kuma ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Shin hukumomi a shirye suke don magance irin wadannan kalubale a koda yaushe, kuma wasu matakai yakamata a dauka don kaucewa aukuwar irin wannan al’amari a gaba?
Karin bayani akan VOA Hausa: https://www.voahausa.com
Karin bayani akan Facebook:   / voahausa  
Karin bayani akan Instagram:   / voahausa  
Karin bayani akan Twitter:   / voahausa  
Karin bayani akan Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci: https://bit.ly/3ElbQit

Shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryam Amurka (VOA) wadanda suka hada da na rediyo, talabijin, shafin yanar gizo da kuma kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram, Twitter da YouTube. Shirye-Shiryenmu sun hada da Taskar VOA da Labarun Mako da Dardumar VOA da Duniyar Amurka da kuma Lafiyarmu.

Sun kan kai ga mutum sama da miliyan 17 da ke bibiyar kafar a kasashen Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi, Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Benin. Sashen kan gabatar da labarai da dumi-duminsu, da batutuwan da suka shafi fashin baki, siyasa, kimiyya, fasahar zamani, kiwon lafiya, kasuwanci da nishadi tare da hadin gwiwar abokanan hulda na gidajen rediyo da talabijin sama da 100 a wasu yankunan Afirka.

show more

Share/Embed