Auratayya 1: Manufar Yin Aure | Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
131K subscribers
17,221 views
624

 Published On Premiered Sep 14, 2022

Dalilai 10 daga Alkur’ani, hadisai da maganganun magabata

1.Fadin Allah cewa Aure ya fara daga kan Annabawa.

2.Fadar Allah (S.W.T)“ku aurar
da marasa aure daga cikinku, da kuma nagartattu daga cikin bayinku maza da kuma bayinku mata”.

3. Ku auri abinda ya dadada muku daga mata, biyu-biyu, uku-uku, hudu-hudu, idan kunji tsoron baza kuyi adalci ba ku wadatu da guda daya”.

4.”Ya ku mutane kuji tsoron Allah wanda ya samar daku daga rai kwaya daya, daga kuma rai kwaya dayan nan ya halitta masa matarsa, domin ku sami nutsuwa izuwa gareta”.

5.Hadisin Anas Bin Malik, wanda wasu sahabbai su hudu suka tambayi Nana Aisha (R.A) yadda Annabi (S.A.W) yake gudanar da ibada, da aka fada musu sai suka ga kamara tayi kadan. anke shawara. Sai na farko yace na dorawa kaina azumi kullum bazan yi fashi ba, na biyu yace kullum da dare zan rika kwana ina Sallah, na uku yace zan kauracewa mata har abada bazanyi aure ba.

6.Hadisin Makal Bin Yasar Annabi (S.A.W) yace “ku auri mai soyayya, mai haihuwa domin zan yawaici al’ummatai ranar alkiyama.

Ammar Bin Yasir, yace Annabi (S.A.W) yace mana “Ya ku dandazon matasa wanda ya samu iko a cikinku yayi aure, domin shi yafi kai matuka wajen runtse ido da kuma kiyaye gaba. Wanda bai samu iko ba to ya shagsla da yin azumi”

8.Abu zarr, Annabi (S.A.W) yace “idan mutum yayi mu’amalar aure da matarsa to Allah (S.W.T) zai rubuta masa ladan sadaka”

Abdullahi bin Amr Bin Al-as. Annabi (S.A.WJ yace “..mafi jin dadin duniya, Allah ya baka mace ta kwarai…”
Sa’id bin Jubair yace “Abdullahi bin Abbas yacemin kayi aure.? Sai nace masa a’a banyi aure ba, sai yace kayi aure. Domin mafi alkhairin wannan al’umma shine wanda yafi yawan iyali”.

show more

Share/Embed